A wannan rana ta Lahadi 11/4/2021 maigirma Sanatan Kano ta tsakiya, Sardaunan Kano Mallam Ibrahim Shekarau, ya shiga karamar hukumar Madobi inda ya kaddamar da aikin hanya da ta dade tana ci wa mutanen yankin tuwo a kwarya.
Inda mai masaukinsa shugaban karamar hukumar Madobi Hon Lawan Yahaya ya rufa masa baya, wannan aikin hanya za'a gudanar dashi ne a karkashi aikin constituency projects da Sanatan Kano ta tsakiya ya kawo, kuma ma'aikata ayyuka ta tarayya zata gudanar akan kudi Naira miliyan 200
Hanyar wacce ta tashi daga gadar 'Yandanko, Kwanar-Zara, Kaurar-Mata da kuma Garu a karamar hukumar ta Madobi

Nan gaba kadan, akwai wasu ayyuka irin wadannan da za su biyo baya a sauran kananan hukumomin dake karkashin wannan constituency na
Kanobta tsakiya karkashin kulawar maigirma Sanatan Kano ta tsakiya Sanata Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano da izinin Allah. http://s4snewsteam.wordpress.com 
You can follow @fanshekara.
Tip: mention @twtextapp on a Twitter thread with the keyword “unroll” to get a link to it.

Latest Threads Unrolled: