A fatawar marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi Rahimahullah, akan ganin wata yace, kasashen dake gabas idan suka riga ganin wata, ya halatta kasashen dake yamma suyi aiki da ganin watan mutan gabas.
Amma idan kasashen dake Yamma suka ga wata alhali wadan da suke gabas basu gani ba, to ba lallai ne mutanan gabas subi ganin mutanan Yamma ba.
Ba mune ya kamata mu fara gani ba domin kafin rana ta fadi anan yankinmu ta fadi acan gabas, to tayaya zamu riga su ganin wata alhali suna gaba da mu da awa biyu ko sama da haka?
Akan wannan batu babu wani Abin cece kuce, domin wadan da suke Gabas ya kamata su rigamu ganinsa, tunda rana tana riga faduwa acan, sai basu gani ba, a bisa yakini in basu gani ba, muma akwai yuwuwar ba zamu gani ba.
Kamar yadda Gabas suke fara ganin hudowar rana, haka suke Fara ganin jinjirin wata lokacin da aka haife shi.

Imamu Malik, da Imamu Ahmad Allah ya yarda da su, cewa suka yi, idan mutum yaga wata da idonsa kuma ya gayawa shugaba, sai Shugaba yaki gamsuwa da ganin watansa,
to tilas wannan mutum yabi umarnin shugaba yayi Azumi ko da yaga watan Shawwal da idonsa.

Shugaba ko yayi hukunci bisa kuskure ba za a tuhume shi ba, kuma hukuncisa daidai ne. To meye abin cece kuce?
Ko da wasu sunga wata Sultan yace bai gamsu da ganinsu ba, to akwai kuskure a Shariah Kan haka?

Wanda duk bai gamsu da yin Azumi yau ba, yaci ya sha yayi Sallar idi ma in yaga dama, to wa ya yiwa? Amma dole a ransa ya san cewar yau ba ranar Sallah karama bace.
Mu kam Mun ji kuma Mun bi. Allah ya taimaki Sultan ya Kara masa imani da kana'a, Allah ya bamu dacewa. Ramadhan Kareem!

Yasir Ramadan Gwale
22-05-2020
You can follow @el_uthmaan.
Tip: mention @twtextapp on a Twitter thread with the keyword “unroll” to get a link to it.

Latest Threads Unrolled: